‎Rike Kannen Zomo: Majalisar Dokokin Kano na Shirin Ladaptar da Dan Majalisar K/H Nasarawa

Date:

‎ Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ce za ta gudanar da bincike kan wani abu da ake zargin ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Nasarawa, Engr. Bello Aliyu, ya wallafa a kafafen sada zumunta, wanda ake zargin ya ƙunshi cin mutuncin majalisar da matsayin da yake riƙe da shi.
‎
‎Matakin ya biyo bayan wani kudiri na gaggawa da ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Minjibir, Alhaji Abdulhamid A. Minjibir, ya gabatar a zauren majalisar yayin zaman majalisar na wannan rana.

IMG 20260704 WA0007
Talla

‎
‎A A Minjibir ya buƙaci a ɗauki matakan da suka dace domin hana sake faruwar irin wannan lamari a nan gaba.
‎
‎daga cikin ’yan majalisar da suka goyi bayan ɗaukar matakin akwai Mai Tsawatarwa na majalisar, Hon. Mudassir Zawaciki, da Shugaban Marasa Rinjaye, Usman Tasi’u Abubakar Kiru.
‎
‎Sauran sun haɗa da ɗan majalisa mai wakiltar Takai, Dr. Musa Ali Kacako, da takwaransa na Madobi, Sulaiman Muktar Ishaq.
‎
‎A ƙarshe, majalisar ta umarci Kwamitin Ladabtarwa da ya gudanar da cikakken bincike kan lamarin cikin gaskiya da adalci, tare da miƙa rahotonsa ga majalisar kafin ko a ranar Laraba, 21 ga Oktoba, 2026.
‎FB IMG
‎

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ra’ayi: Shin Sarki Sanusi ya na amfani da matsalar Kofar Mata domin dakile burin gwamnan Abba na wa’adi na biyu ?

Ra'ayin Muhammad Izzudden MusaWasikar da Sarki Muhammadu Sanusi II...

Kwankwasiyya ta zargi gwamnatin Kano da yunƙurin ciyo bashin Naira biliyan 55 ga kananan hukumomi

Kungiyar Kwankwasiyya ta bukaci Gwamnatin Kano ta yi karin...

Kungiyar Kwankwasiyya ta fitar da jadawalin bukukuwan cikar Kwankwaso shekaru 70 ‎ ‎

‎ ‎‎Ƙungiyar Kwankwasiyya za ta gudanar da bukukuwan murnar cika...

‎Gwamnatin Kano Ta Sha Alwashin Magance Matsalolin ’Yan Kasuwa – Waiya

‎ ‎Kwamishina Waiya ya tabbatar da cewa gwamnati za ta...