Daga Rahama Umar Kwaru
Dan takarar kujerar shugaban karamar hukumar aAjingi a jihar kano Hon Bashir Dauda Sadosa Ajingi ya bayyana cewa yana da kyawawan manufofin da zasu inganta rayuwar al’ummar karamar hukumar Ajingi.
“Na tsara manufofin da zan tafiyar da al’amuran mulki na al’ummar karamar hukumar Ajingi, don haka na yiwa al’ummarmu tanadi mai kyau don inganta harkokin Ilimi da lafiya da kuma samawa matasa matasa maza da mata sana’o’i”.
Ho. Bashir Dauda ya bayyana hakan ne yayin da yake zaman da jaridar kadaura24 a Kano.
Badakalar magungunan Kano: Mun fara bincike kuma za mu gurfanar da duk mai hannu – Muhuyi Magaji
Ya ce a matsayinsa na matashi dole zai yi amfani da tsarin da jagoran jam’iyyar NNPP na kasa Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso da gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf suke amfani da shi wajen inganta rayuwar matasa.
” Ka sani a lokacin sanata Kwankwaso, an samarwa da Matasa masu tarin yawa aiyukan yi, wanda ya basu dama suka dogara da kawunansu, yanzu da yawa daga cikinsu tsaya kafarsu har ma suna taimakon wasu, to haka nake so in yiwa matasan karamar hukumarmu ta Ajingi”. Inji Bashir Sadosa Ajingi
Da dumi-dumi: Ogan Boye ya ajiye mukaminsa na Mai baiwa gwamnan Kano shawara Kan Matasa
Ya ce zai kuma tallafawa Mata saboda idan ka taimaki mace daya kamar ka taimaki al’umma ne baki daya, don haka zan rika baiwa mata jari duk wata har sai na karade dukkanin gidajen dake karamar hukumar Ajingi.
Ya kara da cewa idan ya sami takara zai tabbatar al’ummar karamar hukumar Ajingi sun sharbi romon dimokaradiyya kamar yadda ya kamata ba tare da tauye hakkin kowa ba.