‎Shugaba Tinubu na hanyarsa ta komawa Abuja daga Legos

Date:

‎
‎

‎
‎Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai bar birnin Legas zuwa Abuja a yammacin yau, Litinin, bayan shafe kwanaki shida a birnin.
‎
‎Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga ya fitar.

IMG 20260704 WA0007
Talla

‎
‎Idan za a iya tunawa Shugaba Tinubu ya isa Legas ne a ranar Talata, 29 ga Satumba, bayan ya dawo daga hutun shekara-shekara da ya yi a biranen London da Paris.
‎
‎A yayin zamansa a Legas, shugaban ƙasar ya gabatar da jawabi ga ’yan Najeriya a ranar 1 ga Oktoba, domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.
‎
‎Daga bisani a wannan rana, Shugaba Tinubu ya halarci bikin ƙaddamar da shirin fim mai suna “MKO” a Wole Soyinka Centre for Culture and Creative Arts.
‎

FB IMG
‎
‎A ranar Lahadi kuma, Shugaba Tinubu ya kai ziyara ga Sarkin Legas, Oba Rilwan Babatunde Akiolu, a fadarsa ta Iga Iduganran da ke Tsibirin Legas.
‎

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ƴansanda sun gayyaci wani dan siyasa a Kano bisa zargin fito da bindiga a bayyanar jama’a

‎ ‎Rundunar ’yansandan Jihar Kano ta gayyaci ɗan takarar jam’iyyar...

Gwamnatin tarayya ta bayyana Adadin mutanen da hatsarin jirgin sama ya rutsa da su a Ondo

Ministan Sufurin Jiragen Sama na Najeriya, Festus Keyamo, ya...

INEC za ta gana da masu ruwa da tsaki kan zaben 2027

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta...

‎Kawu Sumaila Ya Baje Kolin Ayyuka 102 da ya yi a Kano ta Kudu, Ya Sake Neman Goyon Bayansu a 2027

‎ ‎Daga Maryan Lawan Kwalli ‎ ‎Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu,...