Daga Auwalu Alhassan Kademi
Shugaban kasa Bola Tinubu, ya yi alkawarin sanya jari mai tsoka a fannonin tattalin arzikin Nijeriya, kamar wutar lantarki, sufuri, lafiya, da ilimi domin saukaka wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke ciki a halin yanzu sakamakon cire tallafin man fetur.
A jawabinsa na bikin ranar dimokuradiyya a ranar 12 ga watan Yuni, shugaban ya kuma yi alkawarin karfafa tsarin shari’ar kasar da kuma ci gaba da inganta dimokuradiyya.
Bugu da kari, ya yabawa Moshood Abiola, wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin 1993, bisa jarumtaka, kishin kasa, da kuma imani da akidar dimokradiyya.
Bayan kwanshe makonni a waje, yau Tinubu zai dawo Nigeria,
Da yake amincewa da cewa yan Nigeria na cikin radadin sakamakon cire tallafin, shugaban ya ce, “Ina jin zafin abun da kuke ji, Amma ba yadda muka iya dole mu dauki wannan matakin don ceto kasarmu daga durkushewa.”
“Na yarda da cewa wannan matakin zai sanya al’ummarmu cikin mawuyacin hali , Ina rokon ku kara hakuri, ka cigaba da sadaukarwa don ci gaban ƙasarmu.”