Majalisar Shura ta Darikar Tijjaniyya a Jihar Kano ta bayyana goyon bayanta ga tazarcen Gwamna Abba Kabir Yusuf a wa’adi na biyu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.

Shugaban Majalisar Shurar Darikar Tijjaniyya, Sheikh Sani Shehu Maihula, ya bayyana hakan ne a yayin taron Zikiri da addu’ar kasa na shekara-shekara da darikar ta shirya a Fadar Sarkin Kano.
Sanarwar ta ce Sheikh Sani maihula ya bayyana goyon bayan takarar Abba ne a karo na biyu A Jawabinsa na maraba, wanda dan uwansa kuma kakakin majalisar, Sheikh Ibrahim Shehu Maihula ya gabatar.
A cewarsa, mambobin Majalisar Shurar Tijjaniyya sun cimma matsaya guda cewa za su mara wa Gwamna Abba Kabir Yusuf baya domin ya sake zabarsa a karo na biyu, saboda abin da suka bayyana a matsayin jajircewarsa wajen inganta shugabanci, bunkasa addinin Musulunci da kuma aiwatar da manufofin da suka shafi jin dadin al’umma.
Malamin ya kuma yaba wa gwamnan kan yadda yake tallafa wa harkokin addini, ilimi, lafiya, samar da ababen more rayuwa da shirye-shiryen walwalar jama’a a fadin jihar Kano.
A nasa bangaren, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode wa shugabanni da mambobin Majalisar Shura na darikar Tijjaniyya bisa addu’o’insu da kuma goyon bayan da suka bayyana masa.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin gaskiya, adalci da tsoron Allah, tare da ci gaba da aiwatar da manufofin da za su inganta rayuwar al’ummar jihar Kano.
Har ila yau, gwamnan ya gode wa malamai da shugabannin addinai a fadin jihar bisa addu’o’i da shawarwarin da suke bayarwa, yana mai cewa suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaban Kano.