Kungiyoyin Darikar Tijjaniyya Sun Karyata Ikirarin Mara Wa Gwamna Abba Baya a Kano

Date:

Wasu ƙungiyoyin ɗarikar Tijjaniyya a Jihar Kano sun musanta rahotannin da ke cewa sun bayyana goyon bayansu ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, domin ya yi tazarce

Shugaban Ƙungiyar Gausiyya ta Tijjaniyya a Kano, Sheikh Abubakar Ahmad Darma, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Kano ranar Asabar.

Sheikh Darma ya ce ɗarikar Tijjaniyya ƙungiya ce ta addini mai cin gashin kanta, ba ta da alaƙa da siyasa, kuma ba ta mara wa wani ɗan takara ko ɗan siyasa baya ba.

IMG 20260704 WA0007
Talla

Sai dai ya bayyana cewa kowane dan ɗarikar yana da ‘yancin shiga kowacce jam’iyya ko kuma goyon bayan ɗan takarar da ya ga dama, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya ba shi dama.

Ya ce, “Mambobin ɗarikar suna da cikakken ‘yancin zaɓar wanda suke so su kaɗa wa ƙuri’a a matsayin ‘yan ƙasa masu amfani da haƙƙinsu na dimokuraɗiyya.”

Ya ƙara da cewa, “Tijjaniyya ba ƙungiya ce ta siyasa ba, ƙungiya ce ta addini da ke da miliyoyin mambobi a faɗin ƙasar nan. Saboda haka, a matsayin ƙungiya ba mu mara wa kowa baya ba, ko da yake kowane mamba na da ‘yancin zaɓe da kuma tsayawa takara.”

Majalisar Shurar Tijjaniyya ta bayyana goyon bayanta ga tazarcen Gwamna Abba Kabir

Har ila yau, Sheikh Darma ya tunatar da mambobin ɗarikar cewa wanda ya assasa Tafarkin Fayda, Sheikh Ibrahim Nyass, ya ƙarfafa shiga harkokin siyasa ne domin yi wa al’umma hidima da tabbatar da jin daɗinsu, ba domin neman abin duniya ba.

Ya ce, “Duk wanda ya shiga siyasa saboda abin duniya, to ya sayar da lahirarsa.”

IMG 20260704 WA0005
Talla

A wani ci gaba mai alaƙa da wannan batu, ita ma Ƙungiyar Sufi Political Awareness Forum reshen Kano, ƙarƙashin jagorancin Malam Tuhami Abubakar Adam, ta fitar da sanarwa tana musanta cewa ta ayyana Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin ɗan takararta a zaɓen shekarar 2027.

Ƙungiyar ta bayyana cewa a matsayinta na ƙungiyar mambobin ɗarikar Tijjaniyya, ba ta gamsu da yadda Gwamna Yusuf ya tafiyar da wasu muhimman batutuwa a jihar ba, musamman abin da ya shafi Malam Lawan Triumph.

Sanarwar ta kuma jaddada cewa Majalisar Shura ta Tijjaniyya ƙungiya ce ta addini, ba ta siyasa ba. Ta ce duk wani goyon bayan da wasu mutane suka nuna wa gwamnan ra’ayi ne na kansu, ba matsayar ɗarikar Tijjaniyya ba, domin kowane mamba yana da ‘yancin zaɓar ɗan takarar da yake so.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Majalisar Shurar Tijjaniyya ta bayyana goyon bayanta ga tazarcen Gwamna Abba Kabir

  Majalisar Shura ta Darikar Tijjaniyya a Jihar Kano ta...

Dalibai Sama Da 300 Sun Daina Karatu Bayan Rushewar Makaranta A Wani Gari Dake K/H Bebeji

Al'ummar garin Unguwar Alhaji Tagidadu da ke mazabar Rantan...

An gano masu juna biyu cikin matan da za a yi wa Auran Zawarawa a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta ɗage shirin...