Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta ɗage shirin auren zawarawa da ta shirya gudanarwa bayan gwaje-gwajen lafiya da aka yi sun gano cewa wasu daga cikin matan da aka tsara aura suna ɗauke da juna biyu.
Shugaban Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Jihar Kano (KSACA), Dr. Usman Bashir, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai kan sakamakon gwaje-gwajen lafiyar waɗanda aka zaɓa domin cin gajiyar shirin.

Dr. Bashir ya ce hukumar ta gudanar da cikakken gwajin lafiya ga dukkan waɗanda za su shiga shirin ne domin tabbatar da cewa an gudanar da auren bisa ingantaccen tsarin kiwon lafiya, tare da kare lafiyar ma’aurata da kuma yaran da za a haifa nan gaba.
Ya ce binciken ya nuna cewa wasu daga cikin matan suna ɗauke da juna biyu, lamarin da ya sa gwamnati ta ɗauki matakin ɗage shirin domin sake tantance halin da ake ciki.
Gwamna Abba Ya Umarci EFCC da ICPC Su Sa Ido Kan Aikin Rabon Taki a Kano
A cewarsa, gwamnatin jihar ta sake buɗe damar yin rajista ga mutanen da suka nemi shiga shirin a baya amma ba su samu ba, inda ta bukace su da su sake neman gurbi domin a yi la’akari da su.
Shugaban KSACA ya ƙara da cewa gwaje-gwajen an gudanar da su ne tare da haɗin gwiwar Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, kuma sun haɗa da gwajin cutar HIV da sauran muhimman binciken lafiya.
Ya jaddada cewa irin wannan tsari na tantance lafiya kafin aure yana taimakawa wajen gano matsalolin lafiya tun da wuri, tare da ba da damar ɗaukar matakan da suka dace domin kare lafiyar ma’aurata da iyalansu.
Premier Radio