Gwamna Abba Ya Umarci EFCC da ICPC Su Sa Ido Kan Aikin Rabon Taki a Kano

Date:

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati ta EFCC da Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa da su sanya ido kan yadda za a raba takin zamani na tallafi a fadin jihar domin tabbatar da gaskiya, adalci da rikon amana.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya aikowa Kadaura24 .

Gwamna Abba ya bayar da wannan umarni ne yayin kaddamar da rabon manyan motoci 150 dake dauke da takin zamani na tallafi ga manoma a kananan hukumomi 44 na jihar.

IMG 20260504 WA0036(1)
Talla

Ya bayyana cewa an shigar da EFCC da ICPC cikin aikin ne da nufin tabbatar da cewa takin ya isa hannun manoma na gaskiya, tare da dakile karkatar da shi, boyewa ko wasu hanyoyin amfani da shi ba bisa ka’ida ba.

Wata Ƙungiyar Ta Bukaci Majalisar Kano Ta Binciki Tsohon Mataimakin Gwamna Gwarzo Kan Zargin karkatar da Naira Miliyan 308

Gwamnan ya kuma bukaci shugabannin kananan hukumomi 44 da su gudanar da rabon cikin gaskiya, adalci da rikon amana, yana mai cewa shirin zai taimaka wajen rage kudin noma, kara yawan amfanin gona da kuma inganta samar da wadataccen abinci a jihar.

IMG 20251224 WA0004

Ya yi gargadin cewa duk wanda aka samu da hannu wajen karkatar da takin ko kawo cikas ga shirin zai fuskanci hukunci bisa tanadin doka.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da gaskiya, rikon amana da kuma amfani da dukiyar al’umma yadda ya kamata, yana mai bayyana noma a matsayin ginshikin tattalin arzikin Jihar Kano.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin barin APC: Ganduje ya magantu

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje,...

Zaɓen Fidda Gwanin APC: Kotu ta Fara Sauraron Karar Hafizu Maidaji Ya Kai Chidari

‎ ‎Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta fara sauraron...

Ma’aikatan Radio Kano na karbar horo kan aikin Jarida na zamani

Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada ƙudirin ta na...