Hukumar gudanarwar gidan Rediyon Tech FM dake jihar Kano ta amince da nada Suyudi Isah Jibril Bichi a matsayin sabon Manajan tashar.
Wannan na kunshe ne cikin wata takardar da aka fitar ranar 13 ga Oktoba, 2025, wacce Manajan Darakta na kamfanin, Mukhtar Tajuddeen Usman, ya sanya wa hannu kuma aka aikowa Kadaura24, inda aka bayyana cewa nadin zai fara aiki nan take.
Suyudi Isah Jibril Bichi yana da Dibloma da digiri na farko (BSc) a fannin aikin Jarida, sannan a halin yanzu yana ci gaba da karatun digiri na biyu (Masters) a fannin hulda da jama’a (Public Relations) a Jami’ar Bayero Kano (BUK).
Suyudi Bichi na da ƙwarewa mai zurfi a harkar yada labarai da aikin jarida, wanda ya samu gogewa ta tsawon shekaru sakamakon aiki da ya yi a kafafen watsa labarai daban-daban.
Kafin wannan mukami, Suyudi Bichi ya rike matsayin Manaja a Guarantee Radio, inda ya shafe shekaru biyu yana gudanar da wannan aiki cikin nasara.