Al’ummar yankin Kunshe a Gwado, da ke mazabar Gandurwawa a cikin karamar hukumar Minjibir ta jihar Kano, sun koka kan rashin ababen more rayuwa da suka haɗa da hanya, asibiti, ruwan sha da makarantar Boko da ta Islamiyya.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa suna fama da matsalar ruwa, inda su ka ce sai sun yi tafiyar kusan kilomita biyu kafin su samu ruwan sha ko na sauran amfanin yau da kullum.
Sun kuma ce mata masu juna biyu na fuskantar ƙalubale wajen zuwa asibiti musamman a lokacin haihuwa ko rashin lafiya, lamarin da ke jefa su cikin haɗari.
Wasu daga cikin matasan garin da iyaye mata sun bayyana damuwa kan halin da suke ciki, inda suka roƙi gwamnati ta kawo musu ɗauki cikin gaggawa.
Da wakilinmu ya nemi jin ta bakin shugaban karamar hukumar Minjibir, Hon. Captain Jibrin Nalado, ta wayar hannu bai daga wayar ba. Sai dai ya aika masa da saƙon kartakwana .
Sai dai shugaban karamar hukumar ta Minjibir ya aiko masa da takaitaccen Sako, inda ya ce, “In sha Allah muna ƙoƙari a duk garuruwan da ke fama da irin wannan matsalar.”