‎Sarki Sanusi II ya bayyana hanyoyi 7 da za a magance talauci a Nigeria

Date:


‎Najeriya ta daɗe tana fuskantar matsalolin talauci da hauhawar farashin kaya, da rashin tabbas a harkokin tattalin arziki, kodayake a baya-bayan nan an ɗan amu sauƙi.

‎Duk da kasancewarta ƙasa mai dimbin arziki, akwai miliyoyin ‘yan ƙasar da ke rayuwa a cikin tsananin talauci, inda rashin aikin yi da rashin wadatacciyar wutar lantarki da hauhawar farashin kayayyaki ke ƙara dagula rayuwar al’umma.


‎A wani taron neman mafitar makomar tattalin arziƙin Najeriya zuwa shekarar 2030, wanda ‘News Central’ ta shirya, Sarkin Kano na 16 kuma tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana wasu shawarwari kan yadda za a iya rage talauci a ƙasar.

‎Sarki Sanusi ya jaddada cewa babban mataki shi ne tabbatar da daidaito a ɓangaren tattalin arziki saboda cimma duk wata manufa ta ci gaban ƙasa.

‎Sarkin ya bayar da shawarwari kan hanyoyin da za a bi domin kaucewa talauci a ƙasar kuma sun haɗa da:

‎1. Samar da Ilimin yaya mata

‎2. Daidaiton tattalin arzikin Kasa

‎3. Kayyade farashin Dala


‎4. Tabbatar da ingantaccen tsarin Ilimi

‎5. Samar da wadatacciyar wutar Lantarki

‎6. Jajircewa da Hakuri don samun cigaba

‎7. Inganta hanyoyin kashe kudaden wajen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...