Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga kujerar Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
Kadaura24 ta rawaito cewa Yakubu, wanda aka nada a shekarar 2015, ya yi wa’adin shekaru biyar sau biyu a ofis.
A ranar Talata, ya mika ragamar shugabanci ga May Agbamuche, kwamishina a hukumar, wacce za ta rike mukamin a matsayin mai rikon kwarya.
Tsohon shugaban hukumar ya roƙi tsofaffin abokan aikinsa da su baiwa mai rikon kwaryar cikakken hadin kai har zuwa lokacin da za a nada sabon shugaban hukuma na dindindin.
Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sanar da sabon shugaban hukumar zabe a kowanne lokaci daga yanzu.