Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ne zai jagoranci tawagar ƙasar zuwa taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) karo na 80 da za a yi a watan nan, a cewar fadar shugaban ƙasa.
Hakan na nufin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba zai je taron ba, kuma wannan ne karo na biyu a jere da Shettima ke jagorantar tawagar ta Najeriya zuwa taron.
Sai dai fadar ba ta faɗi takamaiman dalilin da ya sa Tinubu ba zai je taron ba, wanda shugabannin ƙasashen dunya ke halarta duk shekara a hedikwatar MDD da ke birnin New York na Amurka.
An Yanka ta Tashi Game da Digirin Girmamawar da aka Baiwa Rarara
Wata sanarwa daga ofishin mataimakin shugaban ta ce Shettima zai bi sawun takwarorinsa na ƙasashen duniya wajen tafka muhawara a zauren daga ranar Talata zuwa Lahadi 28 ga watan Satumba.
Amma sai a ranar Laraba Shettima “zai gabatar da jawabin Najeriya a tsakanin ƙarfe 3:00 zuwa 9:00 agogon New York”, in ji sanarwar.

“Bayan kammala taron UNGA, mataimakin shugaban zai wuce Frankfurt na ƙasar Jamus, inda zai gana da jami’an Bankin Deutche kafin ya dawo Najeriya.”