Gwamna Abba Kabir ya sake ɗaukar Malamai sama da 4,000 aiki a Kano

Date:

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ɗauki malamai 4,315 aiki daga cikin tsoffin malamai masu aikin sa kai na BESDA domin su zama cikakkun ma’aikatan din-din-din .

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya aikowa Kadaura24 ranar Alhamis.

Ya ce, Gwamna Yusuf ya mika takardun ɗaukar aiki ga sababbin malamai a filin wasa na Sani Abacha, inda ya shawarce su da su kasance masu kishin aiki, gaskiya, da kuma baiwa dalibansu tarbiyya ta gari.

Ya ce a baya gwamnatin sa ta ɗauki malamai 5,500 a shekarar 2023, sai a shekarar 2024 ya ɗauki Malamai 5,632, yanzu kuma ya dauki 4,000 a watan Mayu 2025, dukkansu daga cikin shirin koyarwa na sa kai na BESDA.

Gwamnan ya ce wannan tsari alama ce ta jajircewar gwamnatinsa wajen gyara harkar ilimi a jihar Kano.

Don ƙarfafa tsarin ilimi, Gwamnan ya sanar da ɗaukar karin malamai 2,616, da kaddamar da shirin daba lamunin ababen hawa na Naira miliyan 200, tare da amincewa da rabon babura 444 da kwamfutoci 300 domin inganta kula da makarantu.

FB IMG 1753738820016
Talla

Haka kuma, ya bayar da umarnin sake buɗe makarantar kwana ta Shehu Minjibir wacce za ta fara da ɗalibai 180, da ɗaukaka darajar wata makaranta a karamar hukumar Ungogo zuwa makarantar kwana, sannan ya amince da ɗaukar masu gadi 17,000 a makarantu a fadin jihar.

Gwamna Yusuf ya jaddada cewa gyare-gyaren ilimi da gwamnatin sa ke aiwatarwa sun fara haifar da ɗa mai ido, inda aka yi la’akari da nasarar da Ɗaliban Kano suka samu a sakamakon jarrabawar NECO ta 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar ODPMNigeria ta shirya taron tattaunawa da matasa a Bichi

Daga Ahmad Isa Getso   Ƙungiyar Rajin Kawo Sauyi da Cigaba...

Yadda Dansanda ya harbe kansa da bindiga a Kano

Wani jami’in dansanda mai suna Aminu Ibrahim ya rasa...

Hukumar jin daɗin alhazai ta Kano ta sanar da kuɗin aikin hajjin badi

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta amince...

Kudade: Ganduje ya caccaki Gwamnatin kano

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Tsohon shugaban jam’iyyar APC...