NNPPn Kano ta bayyana matsayar Kwankwaso kan batun yi wa Tinubu mataimaki a 2027

Date:

Shugabanin bangarori biyu na jam’iyyar NNPP a jihar Kano, Hashimu Dungurawa da Sanata El-Jibril Doguwa, sun gargadi masu sanya tsohon gwamnan jihar, Rabiu Kwankwaso, cikin dambarwar da ake yi kan wanda zai yi wa Bola Tinubu takarar mataimakin shugaban kasa a 2027.

Sun kuma musanta rahoton cewa Kwankwaso na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

A ’yan kwanakin da suka gabata ake ta cece-ku-ce, ta yadda wasu masana harkokin siyasa ke hasashen Kwankwaso.ka iya koma APC har a ba shi takarar mataimakin Shugaba Tinubu a 2027.

InShot 20250309 102512486
Talla

Hasashen ya kara karfi ne a ranar Juma’a bayan murabus din da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya yi, wanda da yawa ke cewa hakan ta faru ne saboda Kwankwaso zai da koma jam’iyyar APC .

Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance daga fadar shugaban kasa ko kuma jam’iyyar APC dangane da wa zai yiwa Tinubu takarar mataimaki a zabe mai zuwa, amm wasu masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa komawar Kwankwaso APC na daga cikin dabarun da Tinubu ya ke bi wajen samun kuri’u a yankin Arewa maso Yamma a 2027.

Sai dai a wata tattaunawa daban-daban da suka yi da ‘yan jaridu a ranar Asabar, Shugabannin bangarori biyu na NNPP sun yi gargadin kan masu yada wancan labari.

A Gaggauce: Fadar shugaban Kasa ta musanta murabus din Sakataren gwamnatin tarayya

Sun bayyana cewa, duk da cewa shugaban nasu ya cancanci ya yi takarar mataimakin shugaban kasa, amma tada batun a wannan lokaci na iya haifar da dambarwar siyasa a kasar.

Doguwa ya bayyana cewa duk da cancantar Kwankwaso na tsayawa takarar VP, bai kamata a tursasa Tinubu kan yin gaggawar yanke shawarar wanda zai yi masa takarar mataimaki a zaben mai zuwa ba, yana mai gargadin cewa yin hakan na iya haifar da matsala.

“Kwankwaso na iya rike kowane mukami na siyasa a kasar nan, ko shakka babu, amma kada mu matsawa shugaban kasa ya yanke shawarar da ka iya zama Kuskure a kasar nan”.

A nasa bangaren, Dungurawa ya bayyana rade-radin da ke alakanta Kwankwaso da APC a matsayin farfagandar siyasa mara tushe.

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

“Babu irin wannan yunkuri, Kwankwaso ba zai shiga APC ba,” in ji shi.

 

Dungurawa ya kuma jaddada cewa Kwankwaso ƙwararren dansiyasa ne, inda ya ce hakan ce ta sa ake yawan hasashe da danganta shi da takarar Mataimakin Shugaban kasa a 2027.

“Yawancin wadannan hasashe da ake yiwa Kwankwaso ana yin su ne saboda mutunci da kuma fatan alheri da shugabanmu ya gina a tsawon lokacin da ya gabata,” in ji Dungurawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan Amincewar Kasar Saudia , an Sanya Ranar Binne Aminu Dantata a Madina

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid...

Rashin Alhaji Aminu Dantata Babban Rashi ne ga harkokin kasuwanci a Duniya – Salbas

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Babban kamfani a masana'antar mai a...

A Gaggauce: Fadar shugaban Kasa ta musanta murabus din Sakataren gwamnatin tarayya

Daga Rahama Umar Kwaru Fadar shugaban Kasa ta musanta labarin...

Gawuna ya mika ta’aziyyar rasuwar Alhaji Aminu Dantata

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna...