Rasuwar Alhaji Aminu Dantata ta bar gibin da zai yi wuyar cikewa a Nigeria – Alhaji. Kabiru Sani Kwangila

Date:

Shugaban kamfanin gine-gine na SKY Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai khadimun Nabiyyi ya bayyana alhini da jimamin sa bisa rasuwar dattijo kuma hamshakin ɗan kasuwa Alhaji Aminu Dantata, da ya rasu yana da shekaru 94 a duniya.

Cikin saƙon ta’aziyyarsa, khadimun Nabiyyi ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai ƙima wanda ya taka rawar gani wajen habɓaka tattalin arziki, bunkasa ilimi, da kuma samar da ayyukan jin ƙai a ƙasar nan, yana mai cewa rayuwarsa tana cike ne da hidimtawa al’umma da kuma kyawawan dabi’u abun koyi ga kowa.

InShot 20250309 102512486
Talla

“Alhaji Aminu Dantata mutum ne da ya sadaukar da dukiyarsa da lokacinsa wajen tallafa al’umma, musamman marasa ƙarfi, kuma ya kasance shugaba abin koyi ga matasa da sauran al’umma.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Kamal Yakubu Ali ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

Aminu Dantata ya bar mana wasiyyar inda za a binne shi – Iyalansa

Ya ƙara da cewa marigayin ya bar babban gibi da zai ɗau lokaci kafin a cike shi, amma abubuwan alheri da ya gudanar a lokacin rayuwarsa za su ci gaba da haskaka tunanin al’ummar Jihar Kano da ma kasa baki daya.

Khadimun Nabiyyi ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, da al’ummar Jihar Kano da kuma dukkan ‘yan Najeriya baki daya, yana roƙon Allah Madaukakin Sarki da Ya jikansa da rahama Ya kuma baiwa danginsa haƙurin jure wannan babban rashi.

Ya kuma yi fatan Allah Ya jikansa da rahama, Ya sa Aljannah Firdausi ce makomarsa da sauran al’ummar musulmi baki daya. .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Nijeriya ta yi babban rashi: Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Aminu Dantata

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya...

Sanarwa ta Musamman daga majalisar malaman Kano game da rasuwar Dantata

SANARWA MUHIMMIYA (GABATAR DA SALLATUL GA'IB) Assalamu Alaikum Warahmatullah, Sakamakon rasuwa...

Aminu Dantata ya bar mana wasiyyar inda za a binne shi – Iyalansa

Iyalan marigayi Alhaji Aminu Alassan Dantata sun shaida cewa...

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...