Daga Sadiya Muhammad Sabo
Yan uwan wata mata da ta rasu bayan ta haihu a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) sun zargi Asibitin da sakacin rashin kayan aiki na na’urar sakatar iskar oxygen, wanda hakan yasa yar uwarsu ta mutu.
Wacce ta rasun mai suna Amina Muhammad Aliyu Gumel, an kwantar da ita a ranar Juma’ar da ta gabata a asibitin bayan da ta kai kanta bayan ta fara jin alamun matsala.

Mahaifiyarta Bilkisu Mukhtar ta ce Halin da take ciki ya tsananta ne jim kadan bayan da aka yi mata tiyatar (CS), sai dai ana zargin asibitin ya kasa baiwa mara Lafiyar kulawar da ta dace.amsa mai kyau dangane da tabarbarewar lafiyarta.
Da ta ke zantawa da SolaceBase a ranar Litinin, Bilkisu ta bayyana abin da ya faru a matsayin mai ban tsoro. Ta ce tun da farko an jinkirta yi wa yarta ta tiyatar saboda likitoci sun dage cewa dole sai an samo jini saboda ko bukatar hakan za ta taso a lokacin aikin ko bayan aikin.
Fada daba: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf – Daga Zainab Nasir Ahmad
A ƙarshe, an gudanar da aikin, amma yanayin jikin Amina ya tsananta bayan an yi tiyatar.
“Da kyar ta ke numfashi. Tabbas mun fahimci tana bukatar taimakon gaggawa, amma likitocin ba su yi gaggawar daukar mataki ba,” in ji mahaifiyar.
A cewar iyalan marigayiyar, an sa wa Amina tsohuwar na’urar iskar oxygen , daga baya kuma aka sa mata na’urar Mai amfani da lantarki amma kuma babu wutar lantarki da za ta iya kunna na’urar.
“Muna kallon yadda take ta faman shan wahalar yin nunfashi, ba ta iya yin komai, sai fanka mai caji mu ka rika amfani da ita saboda zafi ga kuma rashin isashshiyar iskar oxygen,” in ji Bilkisu.

Da aka tuntubi babban jami’an yada labarai ta Asibitin AKTH, Hauwa’u Inuwa Dutse, da farko ta shaida wa SolaceBase cewa tana bukatar a bata lokaci domin ta bincika halin da ake ciki.
Bayan sake kiranta, ta ce tuni hukumar Asibitin ta duba fayil din marigayin, kuma ana ci gaba da bincike don tabbatar da zargin yan uwan mayar.
‘’ Asibitin na gudanar da bincike kan lamarin kuma nan gaba kadan za ta bayyana wa jama’a abin da ya gano.
Hauwa ta kara da cewa “‘yan uwan marasa lafiya ba su da hurumin bayyana hanyoyin da za a bi wajen Kula da majinyaci a cikin asibitin, amma muna daukar duk wani zargi da muhimmanci,” in ji Hauwa.
“Na nemi bayani daga ƙungiyar likitocin. Suna nazarin fayil ɗin majiyyaciyar kuma za mu ba da cikakkun bayanai ga jama’a,” in ji ta.