Daga Abdulmajid Habib
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta haramta duk wasu hawan Sallah a fadin jihar saboda barazanar tsaro.
A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro, rundunar ‘yan sandan ta taya al’ummar Musulmi murna tare da kiran su bi doka da oda.

Sanarwar ta ce an dauki wannan matakin ne bayan tuntubar dukkanin masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a Kano, inda aka sami rahoton cewa wasu sun shirya yin amfani da Hawan Sallah domin kawo tashin hankali a Kano.
Hawan sallah : Sarki Sanusi ya umarci hakimai su shigo cikin birnin Kano
” Ba a yarda a ga kowa akan doki a yayin bukukuwan sallah ba , sannan ba za mu lamunci tseren doki ko mota ba, duk kuma wanda aka samu doka za ta yi aiki a kan sa.
Wannan sanarwar dai na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi ya fitar da sanarwar gayyatar hakimai da mahaya dawakai domin halartar bukukuwan babbar Sallah da ake gudanarwa duk shekara.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito shekara guda Kenan ana Hana yin hawan Sallah a Kano , kuma hakan ya samo asali ne daga lokacin da Rikici ya Barke a Masarautar Kano, inda Sarki Aminu Ado Bayaro da Sarki Muhammadu Sanusi II kowannensu ke da’awar shi ne Sarkin Kano.