Hawan sallah : Sarki Sanusi ya umarci hakimai su shigo cikin birnin Kano

Date:

Majalisar Masarautar Kano ta fitar da wata takarda mai dauke da umarni ga dukkan Hakimai da ‘Yan Majalisa na masarautar da su hallara a Birnin Kano domin halartar bikin hawan Babbar Sallah da za a gudanar cikin makon gobe.

IMG 20250415 WA0003
Talla

A wata takardar sanarwa da Sakataren Majalisar Masarautar Kano, Alhaji Abba Yusuf Danmakwayon Kano ya rattabawa hannu, an bukaci Hakimai da sauran shugabannin gargajiya da su iso Kano tare da dawakan su da mahayan su a ranar Laraba, 8 ga Dhul Hijjah, 1446 Hijira, wanda ya yi daidai da 4 ga Yuni, 2025.

Yadda kamfanin ganyen shayi na Z&Y ke fuskantar matsin lamba daga TOP TEAA

Bayan haka, ana sa ran za su halarci Fadar Mai Martaba Sarkin Kano a ranar Alhamis, 9 ga Dhul Hijjah, wato 5 ga Yuni, 2025 da misalin karfe 11:00 na safe, domin karbar umarni da bayani kai tsaye daga Sarkin Kano. Daga nan kuma za a gudanar da wani taro da Hakimai a dakin taron Majalisar Masarauta dake Kofar Kudu, inda za a fayyace tsarin gudanar da hawan Babbar Sallah na bana.

InShot 20250309 102403344

Majalisar ta kuma tabbatar da cewa an tuntubi shugabannin kananan hukumomi domin saukaka shigowar Hakiman daga yankunansu zuwa Birnin Kano.

A karshe, majalisar ta roki Allah da ya sanya a gudanar da bikin Babbar Sallah cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...