Wani matashin ɗan kasuwa daga jihar Kano, mai suna Yusuf Imam Yahaya, ya fito tare da shaidawa Duniya yadda ya kwashe kusan shekaru shida yana fuskantar abinda ya kira zalunci, rashin adalci, da kuma ƙoƙarin murƙushe kamfaninsa da wasu masu iko ke ko karin yi ta hanyar amfani da kuɗi da wasu marasa kishin kasa.
Yusuf mai shekaru 27 da haihuwa, ya bayyana cewa kamfaninsa dake samar da ganyen shayi na Y&Z ya faɗa cikin rikici da wani babban kamfani da ake kira Top Tea, rikicin da ya samo asali daga tambarin samfurin shayin da kamfaninsa ke sarrafawa duk da cewa sun bi dukkan matakan doka da aka shimfiɗa.
“Mun bi duk hanyar da doka ta tanada,” in ji Yusuf. “Mun yi rijista da CAC (Hukumar Rijistar Kamfanoni), mun samu lasisin tambari daga hukumar Trademark bayan an bincika aka tabbatar cewa ba kowa ke da shi ba. Mun kuma samu takardar amincewa daga NAFDAC da SON kafin mu fara sarrafa ganyen shayin.”
Ya ƙara da cewa kamfanin Z&Y black tea bamu ƙirƙireshi domin son zuciya ba, munbi duk wata hanya ta doka da ƙa’ida.
Duk da bin doka da ka’ida, Yusuf ya ce suna fuskantar matsin lamba da tsangwama daga wasu mutane masu ƙarfi daga ciki kasar nan waɗanda ke ƙoƙarin durƙusar da harkarsu ta kasuwanci.
Nasara A Kotu Da Aka Yi Biris Da Ita
Yusuf ya bayyana cewa kotu ta yanke hukunci inda ya samu nasara har aka tabbatar da cewa waɗanda suke kai musu farmaki da bita da kulli ba su da hurumin mallakar tambarin da ake ta ja’inja akai.
“Alƙali ya tabbatar ba su da hurumi a kan tambarin. Amma maimakon su girmama hukuncin, sai suka koma amfani da wata hanya — sun ƙirƙiro labaran ƙarya a jaridu har ma suka jawo Interpol cikin lamarin,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa rundunar yansandan Najeriya ta saka sunansu da hotansu a jerin masu laifi da ake nema ruwa a jallo, wanda hakan kuma ba daidai bane, domin babu wani mummunan laifi da suka aika, domin duk wannan ya faru ne saboda ja’inja da gaskiya a kan tambarin kamfaninmu, ba wani babban laifi muka aikata ba.
“Ba mu sata ba, ba mu cutar da kowa ba. Ba ma mu muka ƙirƙiri tambarin ba — wata ƙwararriyar hukumar talla ce ta tsara shi. Kuma su kansu sun fito sun ce su ne suka ƙirƙira. Amma sai mu ake zalunta.”
Sako Zuwa Ga Arewacin Najeriya
A cewar Yusuf, wannan batu ba kawai rikici ne na kasuwanci ba — yana da alaka da yadda ake ko karin take haƙƙin matasa ‘yan Arewa da ke ƙoƙarin yin wani abu mai amfani agaresu da sauran matasan yankin.
“Wasu daga waje suna zuwa Arewa suna kasuwanci suna samun ribar da ake nema, amma mu mutanen gari, yan kasa, me ake nunawa yatsa ko da mun yi komai cikin doka,” in ji shi.
Yusuf ya gargaɗin cewa idan aka ci gaba da barin irin wannan zalunci yana faruwa, zai hana matasa tsayawa da kafafunsu su kafa kasuwanci, kuma hakan zai ƙara tsananta fatara da rashin aiki a yankin Arewa.
“Yaushe ne za mu daina kuka cewa ba aikin yi a Arewa, idan waɗanda ke ƙirƙirar aiki ana murƙushe su? Muna da ma’aikata fiye da 500, da iyalai da suka dogara da su. Idan an lalata kamfaninmu, ai rayuwarsu ma za ta lalace.”
Kiran Neman Goyon Bayan Jama’a
Duk da matsin lamba da muke fuskanta, Yusuf ya ce shi da ɗan uwansa, wanda ke da shekaru 29 a Duniya ba za su ja da baya ba.
“Mun kafa wannan kamfanin ne domin gina al’umma, mu nuna cewa matasan Arewa ma za su iya, ba sai mun koma roƙon gwamnati ba. Za mu tsaya tsayin daka mu kare abinda muka gina.”
A saboda haka muna roƙon hukumomin tarayyar Najeriya, kafafen yaɗa labarai, da shugabannin al’umma, tare da rundunar yansandan Najeriya su tabbatar da cewa adalci ya wanzu, ba tar da an takure masu fasaha da burin cigaban ƙasa ba.