Sarkin Musulmi ya umarci yan Nigeria su fara duban watan Zulhijja

Date:

Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ta bukaci al’ummar Musulmin Nigeria da su fara duban jinjirin watan Zulhijja na shekara ta 1446.

 

“Gobe talata 27 ga watan mayun 2025, ita ce daidai da 29 ga watan Zulqida shekara ta 1446 don haka ita ce ranar da za a fara duban jinjirin watan Zulhijja na bana”.

Yadda Rikici ya barke tsakanin yansanda da mutanen gari a Kano

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin harkokin addinin musulunci na fadar Sarkin Musulmi Farfesa Sambo wali Junaidu ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.

Sanarwar duk wanda ya ga watan ya sanar da wani basarake mafi kusa da shi domin mika sanarwar ga fadar mai alfarma Sarkin Musulmi domin tantancewa.

Kadaura24 ta watan Zulhijja dai shi ne wata na karshe a kalandar addinin musulunci, kuma a watan ne al’ummar Musulmi suke zuwa garin Makka domin gudanar da Ibadar aikin Hajji

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...