Shirin bunkasa Noma da Kiwo na Kano na dab da kammala aiyukan hanyoyi a karkara

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Shugaban shirin bunkasa noma da kiwo na jihar Kano, KSADP, Malam Ibrahim Garba, ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba za a kammala aikin hanyoyin karkara na kilomita 70 da aikin shirin ke yi a wasu sassa na jihar.

“Ana kokarin ganin an kammala wadannan ayyuka a cikin ‘yan makonni masu zuwa”.

IMG 20250415 WA0003
Talla

A wata sanarwa da jami’in yada labaran shirin Ameen K Yassar ya aikowa Kadaura24, ya ce Shugaban shirin na KSADP ne ya ba da tabbacin kammala aiyukan lokacin ya suka ziyarci karama hukumar madobi tare da babbar tawagar shirin da ta zo daga Abuja .

Shirin bukusa noma da kiwo da ake gabatarwa a Nigeria dai bankin ci gaban Musulunci ne yake daukar nauyinsa da tallafin jihohin da ake gudanar da shirin.a

Idan aka kammala ayyukan hanyoyin, za su taimaka wajen saukaka zurga-zurga da samun sauki fitar da kayan noma har ma da bunkasa tattalin arzikin mutanen karkara.

Shugaban shirin ya bayyana cewa an kammala aikin titin Zarewa zuwa Danguzuri wanda gwamnan jihar Kano ya kaddamar, yayin da ake jiran lokacin bude aikin titin Minjibir zuwa Baita. Ya kara da cewa sauran hanyoyin suna kan matakin kammalawa nan ba da jimawa ba.

“A wasu garuruwan da ke da nisa da manyan kasuwanni, baya ga hanyoyin karkara, mun gina manyan cibiyoyin hada-hadar kayan noma guda 20, domin hada manoma da masu sayen kayansu da kuma samar da ayyukan noma, bayan girbi da tallace-tallace”.

InShot 20250309 102403344

Tawagar ta kuma ziyarci cibiyoyin tattara nono a Karfi da ke karamar hukumar Kura, inda Shugaban shirin Ibrahim Garba Muhammad ya bayyana cewa KSADP na da burin gina cibiyoyin tattara madarar nono 100 a fadin jihar, daga ciki har an kammala 40.

“Wannan yana daya daga cikin manyan matakan da muka dauka domin karfafa tsarin kiwo da inganta rayuwar makiyaya a Kano,” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...