Hukumar tace fina-finai ta soke lasisin wasu gidajen wasannin gala 8 tare da Haramta aikinsu a Kano

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

A wani mataki na tabbatar da ana bin ka’idojin doka tare da tabbatar da tsaftace gidajen wasannin nishadi na gala, Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano karkashin jagorancin Alh. Abba El-mustapha ta soke lasisin wasu gidajen wasannin gala har guda 8 bisa samunsu da laifin karya dokokin ta.

A wata sanarwa da jami’an yada labaran Hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar Jim kadan bayan kammala taron da manya jami’in Hukumar.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Abdullahi Sani Sulaiman ya bayyana cewa gidajen wasannin da aka rufe sun hada da

1. HAMDALA ENTERTAINMENT (Ungoggo)
2. LADY J ENTERTAINMENT (SanyaOlu)
3. DAN HAUSA ENTERTAINMENT (Sanya Olu)
4. NI’IMA (Zungeru)
5. ARIYA ENTERTAINMENT ( Abedi sabon gari)
6. BABBANGIDA ENTERTAINMENT (Balatus)
7. HARSASHI ENTERTAINMENT ( Ebedi sabon gari)
8. WAZOBIYA (Sanya Olu)

InShot 20250309 102403344

Abdullahi Sani ya Kara da cewa doka ce ta bawa Hukumar damar saka ido tare da tabbatar da masu gidajen wasanni basu ketare iyaka ba inda ya bayyana cewa dokar ta kara bawa Hukumar damar ladaftar da duk wani gida ko dan wasa data samu da aikata laifi.

Idan ba’a mantaba a kwanakin baya Hukumar tayi gargadi tare da dakatar da wasu gidajen wasannin gala tare da soke lasisin wasu daga cikinsu biyo bayan samun su da laifi.

Abba El-mustapha ya yi kira ga jami’an tsaro dasu cigaba da bawa Hukumar hadin Kai sau da kafa domin tabbatar da ana bin doka yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...