Sarkin Yaƙin Garko, mai kishin al’umma, kuma ɗan jam’iyyar APC, Ambasada Mustapha Salisu Akarami, ya ƙaddamar da gangamin duba lafiyar al’ummar mazaɓar Garko da Raɓa, da ke ƙaramar hukumar Garko, a Kano, su 1400, tare da basu magungunan miliyoyin Kuɗi kyauta.
Ambasada Mustapha Salisu Akarami, ya ce ya ɗauki nauyin ƙwararrun Likitoci, don duba lafiyar mutanen tare da basu magungunan kyauta, domin rage musu wata damuwa bisa halin matsin rayuwa da ake ciki.
An duba lafiyar mutanen ne ranar Asabar, a babban Asibitin ƙaramar hukumar Garko, wanda al’umma suka yi fitar ɗango, aka duba lafiyar su a ɓangaren cututtuka daban-daban, tare da basu magungunan kyauta, da kuma basu shawarwarin yadda za su kula da lafiyar su.

Ambasada Mustapha Salisu Akarami, ya kuma ce yanzu haka yana shirye-shiryen yin zagaye na biyu na gangamin duba lafiyar al’ummar sauran mazaɓun ƙaramar hukumar ta Garko tare da fito da wasu tsare-tsare da za su taimaki mutanen yankin.
Ga hotunan yadda taron duba marasa lafiyar ya gudana