Daga Zakariya Adam Jigirya
Dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da bebeji Abdulmumin Jibrin Kofa ya musanta cewa yana nema kujerar gwamnan jihar Kano ko Sanatan kano ta kudu a zaben 2027.
“Na jima ina bayyanawa karara cewa ba ni da sha’awar tsayawa takarar Sanatan Kano ta Kudu, ko kuma kujerar gwamnan jihar Kano a 2027. Duk da haka, ban yi mamakin yadda ako da yaushe sunana yake zama a sahun gaba akan duk wasu batutuwa irin wannan ba”.

Kadaura24 ta rawaito Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana hakan ne cikin wani sako da ya wallafa a sahihin shafinsa na Facebook .
Ya ce a koda yaushe yana godewa Allah saboda ni’imar da yayi masa a siyasa, ya ce ya ci zaben dan majalisar wakilai karo gudu a jam’iyyu daban-daban, sannan ya rike mukamai daban-daban a matakin majalisa da gwamnatin tarayya.
A Gaggauce: Gwamnan Kano ya dakatar da hadiminsa
“Wadanda suka san ni da kyau sun san cewa duk inda na tsinci kaina a siyasance ko ma a harkokin kasuwanci na kafin na shiga tsiyasa da harkokin koyarwa a jami’a Ina jajircewa don ganin na sami nasara”.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito an jima ana hasashen Abdulmumin Jibrin Kofa zai nemi takarar gwamnan Kano ko Sanatan kano ta kudu.