Tsaffin sojojin Najeriya da suka ajiye aiki su 24 sun mika wuya ga tafiyar kwankwasiyya karkashin jagorancin Madugunta Sanata Rabiu Musa kwankwaso.
Tsaffin sojojin sunce sun rungumi tsarin Kwankwasiyya ne domin bada tasu gudu mowar a zaben 2027 musamman burinsu na ganin Kwankwaso yayi nasara a siyasarsa.

Tsaffin sojojin da suka ajiye aiki a watan Janairu na 2025 bayan wa’adin Shekara 35 suna aiki sun bayyana cikakken goyon bayansu ga akidar Kwankwasiyya.
A Gaggauce: Gwamnan Kano ya dakatar da hadiminsa
A wata ziyara da suka kaiwa sanata Rabiu Musa kwankwaso a gidansa karkashin jagorancin Shugaban hukumar bada tallafin Karatu ta jihar Kano,Dr Kabiru Getso Haruna,ya bayyana ziyarar ta tsaffin sojojin a matsayin wata babbar nasara ga tafiyar kwankwasiyya a Najeriya.
A jawabinsa, Madugun kwankwansiyyar Sanata Rabiu Musa kwankwaso ya yabawa sojojin a bisa sadaukarwa da sukayi lokacin da suke aiki.
“Gashi kun dauki lokaci mai tsawo kun sadaukar Lokacin aiki soja, yanzu kuma kuna so ku sake sadaukarwa a tafiyar Demokaradiya,a dan haka dole a yaba muku”,Inji Kwankwaso.