Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Shugaban Karamar hukumar Wudil Abba Muhammad Tukur ya yi alkawarin tallafawa iyaye domin su sami sukunin aurar da ‘yayansu musamman mata.
“Mun san halin da al’umma suke ciki shi yasa muka dabbaka irin wannan tsarin wanda jagoranmu Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya fara yi a Kano, na tallafawa iyaye domin su sami damar aurar da ‘yayansu”.

Abba Muhammad Tukur ya bayyana hakan ne lokacin da yake mika kayan daki ga iyayen wasu amare guda biyu da suke yan asalin karamar hukumar Wudil.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Shugaban Karamar hukumar Wudil kan harkokin yada labarai Abba Ashiru ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.
Za mu yi aikin hanyar Utai zuwa Kademi – Shugaban karamar hukumar Wudil
Ya ce zai cigaba da duk mai yiwuwa don tallafawa iyayen yara a yankin musamman iyayen yaran da ba su da karfi.
A jawabinsu daban-daban iyayen Amaren sun godewa shugaban karamar hukumar ta Wudil bisa tausayi da imani da ya nuna wajen dauke musu nauyi kayan dakin da ya rataya a wuyansu.
Wadanda aka baiwa kayan dankin dai daya ta fito ne daga mazar cikin garin wudil yayin da guda kuma ta fito daga mazabar utai duk a karamar hukumar Wudil.
Kayan dakin da shugaban karamar hukumar Wudil Abba Muhammad Tukur ya tallafawa amaren da su sun hadar da Gado da katifa, sai kujeru da madubi da fulollata.