Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Hukumar Kula da aikin hajji ta Najeriya ta ce ta kwashe maniyyatan Najeriya 24,744 zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin hajjin shekarar 2025 a cikin kwanaki 10.
NAHCON ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban jami’in yada labaranta, Malam Shafil Mohammed, ya fitar a Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa mataimakin shugaban kasar Kashim Shettima ne a ranar 9 ga watan Mayu, ya kaddamar da fara tashin Maniyatan na jirgin na farko a Owerri, Imo.
Mohammed, ya ce a cikin kwanaki goma, jirage 61 sun yi nasarar jigilar alhazan Najeriya 24,744 zuwa kasar Saudiyya.
A Gaggauce: Gwamnan Kano ya dakatar da hadiminsa
Ya ce hukumar za ta rika sanar da jama’a irin ci gaban da aka samu kan aikin.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, NAHCON wata hukuma ce ta gwamnati da ke tsarawa tare da kula da ayyukan Hajji da Umrah ga Musulman Najeriya don tabbatar da tafiyar hajji cikin sauki da inganci.