Daga Ummahani Abdullahi Adakawa
Dan majalisar dattawa mai wakiltar Kano ta Kudu, Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila, ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya cire tallafin man fetur ba shugaba Bola Tinubu ba.
Kawu Sumaila ya bayyana hakan ne a a wata hira da aka yi da shi yau laraba a shirin Politics Today na gidan Talabijin na Channels TV.

Ya bayyana cewa dama a kasafin kudin shekara ta 2023, da Buhari ya yi ya tanadin kudin tallafin man fetur na zangon farko na shekarar ne kawai.
Gwamnatin Kano ta magantu kan batun sayawa sarki Sanusi motocin Miliyan 670
Ya ce Tinubu ya sanar da cire tallafin ne bayan gwamnatin da ta shude ta rika ta cire.
“Gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta cire tallafin man fetur saboda dama ba ya cikin kasafin kudin shekara, a wannan shekarar an sanya tallafin man fetur ne daga watan Janairu zuwa Yuni, daga ranar ba za a saka ba da tallafin man fetur ba, kawai sanar da cire tallafin man fetur Tinubu amma ba shi ya cire ba”. Inji Kawu Sumaila
Sanata Kawu Sumaila dai bai jima da shiga jam’iyyar APC ba, bayan da ya fice daga jam’iyyar NNPP ta Rabi’u Musa Kwankwaso.