Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin mai girma gwamna, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta kaddamar da wani babban kwamiti da aka dorawa alhakin gudanar da muhimman gyare-gyare a ma’aikatar lafiya ta jihar.
An gudanar da bikin kaddamar da kwamitin ne a ofishin sakataren gwamnatin jiha Alhaji Umar Farooq Ibrahim.

A wata sanarwa da sakataren yada labaran ofishin sakataren gwamnatin jihar Musa Tanko Muhammad ya Aiko Kadaura24, ya ce wannan matakin ya kara tabbatar da kudirin gwamnatin Kano na karfafawa da farfado da tsarin samar da lafiya a fadin jihar Kano.
Gwamnatin Kano ta magantu kan batun sayawa sarki Sanusi motocin Miliyan 670
An dai dorawa kwamitin alhakin gudanar da cikakken nazari kan kalubalen da ke fuskantar cibiyoyin kiwon lafiya mallakar gwamnati musamman batutuwan da su ka shafi rashin isassun kayan aikin likitanci da kuma gibin da ke tattare da ma’aikata. Aikin na su ya hadar da duk kanana da manya asibitoci dake Kano.
A na sa ran kwamitin zai gabatar da shawarwari masu ma’ana wadanda za su bai wa gwamnati damar samar da ingancciyar kiwon lafiya da daukacin al’ummar jihar Kano.
An bukaci al’umma da masu ruwa da tsaki, da ƙwararru a fannin kiwon lafiya da su ba da gudummawa sosai ga wannan shirin ta hanyar gabatar da shawarwari masu ma’ana ga kwamitin.
Gwamnatin jihar Kano ta nanata kudurinta na sake fasalin fannin kiwon lafiya tare da mutunta irin gudunmawar da masu ruwa da tsaki ke bayarwa wajen gina jihar Kano.