Gwamnatin Kano ta magantu kan batun sayawa sarki Sanusi motocin Miliyan 670

Date:

Daga

 

Gwamnatin jihar Kano ta umurci kananan hukumomi 44 da ke jihar da su bayar da gudunmuwar kimanin naira miliyan 15.2 kowacce – jimillar naira miliyan 670 domin siya da gyaran ababen hawa ga majalisar masarautar Kano karkashin jagorancin Sarki Muhammadu Sanusi.

Kamar yadda wata wasika mai dauke da kwanan wata, 25 ga watan Maris 2025, da ke yawo a kafafen sada zumunta ke nunawa, za a cire kudaden ne daga asusun hadin gwiwa na kananan hukumomi sannan a biya wani kamfani mai zaman kansa, Sottom Synergy Resources Ltd. Ana sa ran kamfanin zai samar da sabbin motoci guda hudu tare da gyara wasu tsoffin motoci guda biyu.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Wasikar na dauke da sa hannun Daraktan sa ido na kananan hukumomi, Abubakar S. Dabo a madadin Kwamishinan Ma’aikatar kananan Hukumomin Jihar.

A wani bangare na wasikar na cewa, “An umurce ni da in isar da amincewar Gwamnati na fitar da jimillar kudi Naira miliyan 15,227,272.72 a asusun kowace karamar hukuma domin gyaran motoci biyu tare da siyo karin wasu guda hudu ga Majalisar masarautar Kano wanda kamfanin Sottom Synergy Resources Ltd zai dauki nauyin siyowa.

Za mu kashe sama da biliyan 4 wajen yin aiyukan raya kasa a mazabun Kano -Gwamna Abba gida-gida

Wasikar ta kuma umurci shugabannin kananan hukumomin da su tabbatar an bi tsarin da ya dace wajen aiwatar da wannan umarni.

A tattaunarsa da manema labarai kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya tabbatar da ba da Umarnin, sai dai ya ce Wannan ba sabon abu ba ne a gwamnati.

” Mutane ne suke ta juya abun amma wannan abu ne da gwamnatocin suna yi, kuma dama alhakin kananan hukumomin ne su kula da harkokin Masarautu”.

InShot 20250309 102403344

Ya ce motoci za a sayo su ne domin aikin al’umma kuma Masarauta aka siyasawa ba sarki Sanusi II ba, don haka ya bakaci al’ummar jihar da su dai na ruduwa da irin wadancan zantuka da wasu suke juyawa.

Al’ummar jihar Kano dai na ta tofa albarkacin bakinsu game da wannan umarnin na sawa sarki Sanusi motoci da gyara masa wasu akan kudi Naira Miliyan 670.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...