Rikicin Masarautar kano: Yansanda sun garkame gidan Galadiman Kano

Date:

Kamal Yakubu Ali

 

Rahotanni na tabbatar da cewa jami’an tsaro sun rufe gidan Galadiman Kano da ke unguwar Galadanci a karamar hukumar Gwale.

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa tun cikin daren jiya Alhamis aka hangi jami’an yansanda sun rufe iya kokin Gidan na Galadima.

“Yansandan sun shigo unguwar ne da kusa kimanin karfe 2 na dare, kuma su ka gindawa motocinsu a kofar shiga gidan da kuma sauran muhimmman hanyoyin da za su sada mutum da gidan na Galadiman Kano” . Inji wani mazaunin unguwar

IMG 20250415 WA0003
Talla

Ya ce tun a makon da ya gabata ne sarki Sanusi ya ba da umarnin gyare gidan domin sabon Galadiman da zai nada ya tare a gidan tunda dama gidan sarautar Galadiman Kano ne.

Wannan dai na zuwa ne bayan da ake saran Sarkin Kano Muhammad Sunusi || zai raka Galadiman Kanon da ya nada Mannir Sunusi, bayan na dashi kamar yarda al-adar Masarautar Kano take.

Kungiyar Kwadago ta Kano ta aikewa gwamna Abba gida-gida muhimmin sako

Rikicin Masarautar kano na neman sake dawowa sabo tun bayan mutuwar Galadiman Kano Alhaji Abbas Sanusi, inda Sarki Sanusi II ya nada Munnir Sanusi a matsayin Galadima yayin da shi ma Sarki Aminu Ado Bayero ya nada dan uwansa Alhaji Sanusi Ado Bayero a matsayin Galadima.

InShot 20250309 102403344

Kuma dukkanin wadannan nadin mai cin karo da juna zai gudanar da bukukuwan nadin ne a Wannan rana ta Juma’a, sai Sarki Sanusi za na da na shi Galadiman a fadarsa dake gidan rumfa yayin da Shi kuma Sarki Aminu zai nada na shi Galadiman a fadarsa dake gidan Sarki na Nasarawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...

Ciyaman din Wudil ya kaddamar da aikin gina magudanan ruwa a wasu garuruwa a yankin

Daga Maryam Adamu Mustapha   Shugaban karamar hukumar Wudil, Hon. Abba...