Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyarar aiki ta kwanaki Biyu zuwa jihar Katsina .
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun fadar Shugaban Kasa Bayo Onanuga ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.

Sanarwar ta ce a yayin ziyarar shugaban kasar zai gana da masu ruwa da tsaki domin duba yanayin tsaro a jihar.
Kungiyar Kwadago ta Kano ta aikewa gwamna Abba gida-gida muhimmin sako
Zai kaddamar da cibiyar injinan noma ta Katsina da kuma titin mota mai nisan kilomita 24 wanda Gwamna Dikko Umar Radda ya kammala.
Shugaba Tinubu zai kuma halarci daurin auren diyar gwamnan kafin ya koma Abuja.