Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa ‘yan siyasar arewacin Najeriya sun gaza wa yankin, kuma dole su nemi afuwa daga wajen al’umma.
TheCable ta rawaito cewa da ya ke wata hira da TRUST TV, Uba Sani ya ce sukar gwamnati ya kasance don gina kasa ne ba kawai don son karbar mulki ba.

“A kowace dimokuradiyya, dole a bar mutane su soki gwamnati, amma wannan suka ya zama mai amfani kuma yana da fa’ida ga ‘yan Najeriya. Hakan muka yi lokacin da muke fafutukar kare hakkin al’umma — ba don muna neman mulki ba,” inji shi.
Gwamnatin Kano, za ta kula alakar Noma, kasuwanci da makamashi da kasar Morocco
“Amma idan kana suka ga gwamnati alhali kai ma ka taba rike madafun iko… Kamar yadda na fada, duk wanda ya fito daga arewacin Najeriya kuma ya taba rike wani mukamin siyasa cikin shekaru 20 da suka wuce, dole mu kalli kanmu a madubi mu roki gafara daga al’ummar Arewa. Mun ci amanar su.”
“Dole na fadi gaskiya, dukkan mu, har ni, Nima nayi majalisar dattawa amma har yanzu matsalolin Arewa sun dade su na faruwa kuma har yanzu na gaza magance su,”