Daga Shu’aibu Sani Bagwai
Karamar hukumar Bagwai a jihar Kano ta bayar da kwangilar gina gada a garin Kwajale wadda za ta hada kauyuka bakwai har zuwa karamar hukumar Rimingado, akan kudi sama da Naira miliyan 160.
Kadaura24 ta rawaito Shugaban karamar hukumar Alh. Bello Abdullahi Gadanya ya bayyana haka ne yayin kaddamar da aikin gadar a garin Kwajale.

Ya ce za a kammala aikin gadar ne cikin watanni biyu zuwa uku domin saukaka matsalar sufuri da jama’ar yankin ke fuskanta musamman a lokacin damina .
Gwamnatin Kano, za ta kula alakar Noma, kasuwanci da makamashi da kasar Morocco
Alh. Bello Gadanya ya bayyana cewa idan an kammala gadar gwamnan jihar Kano ya baiwa karamar hukumar tabbacin gudanar da aikin titin mai tsawon kilomita 15 da ya lalace wanda ya hada kauyuka bakwai daga Kiyawa har zuwa karamar hukumar Rimingado.
Shugaban ya yi kira ga al’ummar yankin da su cigaba da mara wa gwamnati baya saboda kokarin da gwamnatin jiha da ta karamar hukumar ke yi na bunkasa rayuwa da tattalin arzikinsu.
Dan kwangilar dake aikin Alh. Musa Ibrahim Badau, ya ce a matsayinsa na dan karamar hukumar ya bada tabbacin gudanar da aikin mai inganci kamar yadda aka yi yarjejeniya da shi.
Shi ma da yake nasa jawabin kansilan mazabar Rufa’i Isa ya yabawa shugaban karamar hukumar saboda gudanar da aikin gadar, inda ya ce sama da shekaru 10 suna bukatar a yi musu aikin amma ya gagara sai a wannan lokaci.