Hukumomi a kasar saudiyya sun bayyana cewa rukunin farko na Maniyata aikin hajjin bana za su Fara isa kasar a ranar 29 ga wannan wata na Afirilu 2025 domin fara ibadar aikin hajji.

Kadaura24 ta rawaito Ana fara ibadar aikin hajji ne a ranar 8 ga watan zulhijja na kowacce shekara.
Babu kamshin gaskiya a zarge-zargen da ake yi min – shugaban NAHCON
Shafin Haramai Sharifain ne ya bayyana hakan a sashin shafinsu na Facebook.
Sanarwar ta ce ana umartar duk wadanda suke gudanar da Umara a kasar da su tabbatar sun kammala sun fice daga kasar kafin ranar 29 ga watan Afirilun 2025.