Shugaban jam’iyyar APC a Kano, Abdullahi Abbas ya yi kira ga jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Rabi’u Musa Kwankwaso da kar ya shigo APC da kungiyar siyasar sa mai suna Kwankwasiyya.
Kadaura24 ta rawaito cewa a kwanan nan akwai raɗe-radin mai karfi cewa Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano, na shirin sauya sheka zuwa APC.

Sai dai kuma da ya ke taron manema labarai a sakatariyar APC ta Kano a yau Juma’a, Abbas ya ce ba ruwan APC da wata ƙungiya ta siyasa cikin jam’iyyar.
Daily Nigerian ta rawaito duk da cewa Abbas bai fadi Kwankwasiyya ba, amma a jawabin nasa ya nuna cewa babu wata kungiya da za ta dake da jam’iyyar siyasa da za a bari ta shigo cikin APC.
Wata kungiya ta bukaci Gwamnan Kano ya dakatar da Shugaban karamar hukumar Gwale
Ya kara da cewa duk masu tururuwar dawowa APC ba za a ki karbar su ba amma sai sun je mazabu su sun yi rijista.
Ya kuma ce dukkanin shugabannin da ke rike shugabancin jam’iyyar a matakai daban-daban a jihar suna nan akan mukaman su.
” Muna sanar da duk wanda yake son shigowa APC cewa kofar mu a bude take, amma ka sani shigowar ka APC ba zai hana a EFCC da ICPC cigaba da bincikarka ba”. Inji Abdullahi Abbas