Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Arewa Solvation Movement ta bukaci gwamnan jihar Kano da majalisar dokokin jihar da su dakatar da Shugaban karamar hukumar Gwale har sai an kammala bincike da ake yi masa a hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon kasa EFCC.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka aikowa Kadaura24, mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na kasa Com. Adamu Sa’ad da sakataren kungiyar Shehu Haruna.

Sanarwar ta ce kungiyarsu ta dauki wannan matakin ne a kokarinta na kare martaba da kimar Arewacin Nigeria da kuma kokarin ganin an yi daidai.
” Bai kamata a bar mutumin da ake zargi da almundahanar kudade cigaba da shugabantar al’umma ba, don haka mu ke ganin ya kamata a dakatar da shugaban karamar hukumar don a ba da dama a yi bincike yadda ya kamata”.
“Kima da martabar Kano da karamar hukumar Gwale ya na da matukar muhimmanci shi yasa muke kira ga gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da majalisar dokokin jihar Kano da su kare kimar Kano da Gwale”. Inji sanarwa
Sanarwar ta ce kungiyar Arewa Solvation Movement ba ta da alaka da wata jam’iyyar siyasa, muna wannan fafutuka ne don kare kimar Arewacin Nigeria.