Daga Rahama Umar Kwaru
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya zama Gwarzon gwamna na shekarar 2024 bisa la’akari da irin gudunmawar da ya bayar a fannin ilimi.
An bayar da kyautar ne a yayin bikin karramawar jaridar Leadership karo na 17 da aka gudanar a dakin taro na Banquet dake fadar shugaban kasa, Abuja.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24, ya bayyana wannan karramawar a matsayin tabbatar da sauye-sauyen da gwamna Yusuf ya yi a fannin ilimi, wanda ya farfado da fannin a jihar Kano bayan shekaru da dama da aka yi watsi da shi.

An yaba wa Gwamna Yusuf musamman kan ware kashi 31% na kasafin kudin jihar ga fannin ilimi, wanda ya zarce bukatar UNESCO, da kuma kafa dokar ta baci a fannin.
Da yake jawabi bayan karbar lambar yabon, Gwamna Yusuf ya nuna godiya ga wadanda suka shirya taron, inda ya bayyana karramawar a matsayin abar alfahari a gare shi
Abba Kabir Yusuf, ya kuma sadaukar da lambar yabonsa ta ‘Gwarzon Gwamna na jaridar LEADERSHIP’ ga yara marasa galihu a yankunan karkara.
Yanzu-yanzu: Sarki Sanusi ya nada sabon Galadiman Kano
Ya ce kyautar za ta ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da kyautata harkar ilimi.
“Za mu ci gaba da jajircewa wajen bayar da ilimi kyauta da samar da duk kayan da ɗalibai ke buƙata, musamman a yankunan karkara,” in ji Gwamna Yusuf a wajen bikin bayar da kyautar a Abuja.
Gwamnan ya ƙara da cewa wannan karramawar za ta zaburar da sauran masu riƙe da muƙaman gwamnati su mayar da hankali kan jin daɗin al’umma da gina dimokuraɗiyya mai inganci.
“Wannan kyauta ba tawa ce ni kaɗai ba, ta dukkanin yaran Kano ce da ke da burin zuwa makaranta. Wannan yana ƙara mana ƙwarin gwiwa mu ci gaba da ƙoƙari,” in ji shi.
LEADERSHIP tana karrama mutane da ƙungiyoyin da suka taka rawar gani a fannoni daban-daban kamar gwamnati, kasuwanci da al’umma.