Yanzu-yanzu: Sarki Sanusi ya nada sabon Galadiman Kano

Date:

Daga Sani Idris maiwaya

 

Mai Martaba Sarkin Kano na 16 Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu ya amince da Alhaji Mannir Sunusi Hakimin Bichi a matsayin sabon Galadiman Kano.

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a ranar talatar data gabata ne Allah ya yiwa Galadiman Kano Alhaji Abbas Sanusi rasuwa, wanda hakan ta ba da damar maye gurbin nasa.

InShot 20250309 102403344
Talla

Sabon Galadiman Alhaji Mannir Sanusi shi ne ya bayyana hakan ga wakilin kadaura24 a ranar talata .

Ya ce Sarki Sanusi II ya amince da nadin ne bayan da ya tattauna da masu ruwa da tsaki na Masarautar, inda daga karshe aka amince Alhaji Mannir Sanusi ya za ma sabon Galadiman Kano.

Babu wata baraka a hukumar NAHCON – Farfesa Abdullah Pakistan

Mannir Sanusi ya kara da cewa Sarki ya kuma amince da nada Turakin Kano A Matsayin Sabon Wamban Kano, yayin da Adam Sanusi aka nada shi a matsayin Tafidan Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...