Da dumi-dumi: Sanata Kawu Sumaila ya kawo aikin sama da Naira Biliyan 120 Kano

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Sanatan Kano ta kudu Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu bisa yadda ya amince da kasashe sama da Naira Biliyan 124 wajen karasa aikin titin Kano zuwa Maiduguri.

Ina mai farin cikin sanar da al’ummar mazabata ta kano ta Kudu da Kano, mutanen Najeriya baki daya, cewa bayan kudirin da na gabatar a kan Sashin farko na titin Kano – Maiduguri da na gabatar a ranar 7 ga Mayu, 2024, Majalisar Zartarwa ta Kasa, karkashin jagorancin Shugaban Kasa, ta dauki kwararan matakai. An soke kwangilar da aka bayar a baya kuma an sake ba da aikin hanyar ga kamfanin Triacter Construction”.

Kadaura24 ta rawaito Sanata Kawu Sumaila ya bayyana hakan ne a sashin shafinsa na Facebook da yammacin ranar talata.

InShot 20250309 102403344
Talla

Ya ce ” An bayar da sabuwar kwangilar ne wadda aka ba da ita akan kudi Naira Biliyan Dari da Ashirin da Hudu, Naira Miliyan Dari Hudu (₦124,400,000,000), kuma an baiwa kamfanin awa’adin shekaru uku domin ya kammala aikin.

“Wannan sashe na titin, wanda ya dade da zama tarkon mutuwa—wanda ke haifar da hadurruka akai-akai, da asarar rayuka, da cunkoson ababen hawa— yanzu zai samu kulawar gaggawa da ya kamata.

Yanzu-yanzu: Sarki Sanusi ya nada sabon Galadiman Kano

Ya ce wannan kundin ya tabbatar da aniyarsa ta kawo ababen more rayuwa ga al’ummarsa don inganta rayuwarsu.

Ya kara da cewa “Ina fatan in mika godiyata ga Majalisar Dattawan Najeriya, da abokan aikina da Ministan Ayyuka, da kuma Maigirma Shugaban Kasa bisa kokarinsu na ganin wannan aikin mai muhimmanci ya tabbata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...