Mun gamsu da yadda malamai da daliban su ka koma makarantu – Gwamnatin Kano

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Gwamnatin jihar Kano ta yaba da yadda ɗaliban makarantun firamare da sakandire suka koma makarantunsu a yau litinin 7 ga watan Afrilu domin fara karatun Zango na uku na shekarar 2025.

Kwamitin da ke sa ido kan makarantun sun bayar da rahoton cewa malamai da daliban makarantun da su ka ziyarta sun koma makarantunsu yadda ya kamata.

InShot 20250309 102403344
Talla

A Wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Kano Balarabe Abdullahi Kiru ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa Malamai da daliban sun fara zuwa makarantun da misalin karfe 7:30 na safe.

Shugaban K/H Dala ya kaddamar da aikin hanya na kusan Naira miliyan 200 a mazabar Gobirawa

“Mun ga yadda malamai suka fara Shirye-Shiryen ba da karatu, tare da tsaftace harabar makarantunsu domin fara karatunsu cikin sauki.” Inji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa kwamishinan ilimi na jihar Dr. Ali Haruna Makoda ya yaba wa mahalarta malamai da daliban, ya kuma bukaci shugabanni da malamai da su kara himma wajen gudanar da aikinsu yadda ya dace.

Ya godewa iyaye bisa hadin kan da suka ba su, ya kuma yi alkawarin gwamnati za ta cigaba da inganta harkar ilimi a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...