Daga Isa Ahmad Getso
Tsohon mataimakin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kano, Hon. Murtala Sule Garo ya bukaci al’ummar Musulmi da su ci gaba da dagewa wajen yin ibadu ko da bayan azumin watan Ramadan.
Garo ya bayyana haka ne a cikin sakonsa na Barka da Sallah da ya aikowa Kadaura24 ranar Asabar a Kano.
Ya taya al’ummar musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan na shekarar 2025 cikin nasara da kuma bukukuwan Sallah.

Galadima Garo ya tunatar da al’umma cewa su cigaba da aiki koyarwar Alkur’ani da Hadisi domin yin hakan zai sake kyuatata zaman lafiya da soyayyar juna da samun yardar Allah S W A.
Ya ce kamata ya yi mutane su dore da yadda su ka rika yin ibadu a cikin watan azumin Ramadan, har tsawon rayuwarsu.
Sallah: Kungiyar RATTAWU a Kano ta sauke kabakin arziki ga ya‘yanta
Da yake godewa Allah da ya nuna masa wannan lokacin, tsohon kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Murtala Sule Garo, ya bayyana cewa bikin sallah ya ta’allaka ne da soyayya, tallafawa mabukata da kuma zaman lafiya da yin abubuwan da ba su sabawa koyarwar addinin musulunci ba.
Garo ya bukaci al’ummar musulmi da su yi amfani da lokutan bukukuwan Sallah domin su yi addu’o’in samun dawwamammen zaman lafiya a Kano da Najeriya baki daya.