Hawan Sallah: Yansandan Kano sun gayyaci hadimin Sarki Sanusi II bayan mutuwar wani

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wani mutum mai suna Usman Sagiru, mai shekaru 20, dan unguwar Sharifai a birnin Kano, da laifin kisan kai da kuma kai wa ‘yan Vigillante hari a yayin da tawagar Sarki Sanusi Lamido Sanusi II ke hanyar komawa gida bayan sallar idi a ranar Lahadi 30 ga Maris, 2025, da misalin karfe 12:40 na rana.

Kadaura24 ta rawaito Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.

Ya ce yayin da tawagar Sarkin ta taho daga filin Sallar Idi, Usman Sagiru da wasu, sun caka wa Surajo Rabiu, Vigillantee daga unguwar Sabon Titi Jaba wuka, wanda daga baya ya mutu sakamakon mummunan raunin da ya samu.

IMG 20250330 WA0005
Sakon Barka da Sallah

Ya kara da cewa, wani dan Vigillante kuma mai suna Aminu Suleman daga unguwar Kofar Mata ya samu raunuka kuma a halin yanzu yana samun kulawar likitoci a Asibitin kwararru na Murtala Mohammed Kano, a yayin da suke kokarin baiwa Sarki Sanusi kariya.

Sarki Aminu da Sarki Sanusi sun bukaci gwamnati ta hukunta duk masu hannu a kisan Mafarautan Kano a Edo

“Rundunar ‘yan sandan ta fara bincike kan lamarin tare da mika goron gayyata ga Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku domin yi amsa tambayoyi.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sake nanata matsayarta na haramta hawan sallah a Kano, sannan ta yi gargadin cewa duk wanda aka samu yana hawan sallah za a hukunta shi, kuma sun ce ba za su lamunci fadan daba ba.

InShot 20250309 102403344
Talla

Ya jaddada cewa duk wanda aka samu da aikata wani abu da zai iya haifar da rashin zaman lafiya ko tabarbarewar doka da oda, to za a kama shi kuma ya fuskanci fushin doka.

Rundunar ‘yan sandan ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu tare da ba ‘yan sanda hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...