Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana aniyarya wajen sauyawa da inganta rayuwar duk wani matashi da yake harkar daba kuma ya zabi ya dai ya koma mutumin kirki kamar yadda yake a baya.
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da yake raba kayan Sallah da tsabar kudi #10,000 ga tubabbun yan daba sama da dari bakwai a jihar, a karkashin wani shirin zaman lafiya mai suna “Safe Corridor”.

Kwamishinan, ya bukaci matasa da su cika alkawuran da suka daukarwa gwamnati na ajiye makamansu, su fita daga harkar ‘yan daba, su guji shaye-shayen miyagun kwayoyi da munanan dabi’u da kuma rungumar zaman lafiya da mutunta rayuwarsu da ta sauran jama’a.
Hawan Sallah: Yansandan Kano sun gayyaci hadimin Sarki Sanusi II bayan mutuwar wani
Waiya ya tabbatar wa da matasan da suka tuba da cewa idan suka cika alkawuran da suka dauka, gwamnatin jihar karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta bullo da shirye-shiryen da za su sauya rayuwarsu ta bangarori da dama.

Tun da farko, fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Nura Arzai, a wani takaitaccen wa’azin da ya yi, ya shawarci matasa da su koma makaranta su kara samun ilimin addinin musulunci da na yamma domin ci gaban rayuwarsu.
Sheikh Nura Arzai ya bukaci matasa da su yi koyi da salon rayuwar matasan da Allah SWT ya yaba musu a cikin Alkur’ani.