Karin haske kan dalilan yansanda na hana Hawan Sallah a Kano

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta haramta duk wasu haye-hayen karama Sallah a bana.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ne ya sanar da dakatarwar a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sandan Bompai, ranar Juma’a.

Bakori ya jaddada muhimmancin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali yayin bukukuwan sallah.

InShot 20250309 102403344
Talla

Ya ce bincike ya tabbatar da cewa akwai yiwuwar samun tashe-tashen hankula idan har aka gudanar da hawan sallah.

“Mun sami sahihin rahotannin sirri dake nuna cewa bata-gari sun shirya yin amfani da hawan sallah wajen kawo tarnaki, rundunar ‘yan sandan bayan ta tuntubi gwamnatin jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki, ta yanke shawarar haramta duk wani Hawan Sallah a fadin jihar,” in ji CP Bakori.

Dalilan mu na Dakatar da Hawan Sallah a Kano – Sarki Aminu Ado Bayero

Kwamishinan ya tabbatar wa mazauna jihar Kano cewa an samar da isassun matakan tsaro don tabbatar da cewa al’umma sun gudanar da Sallar Idi lami lafiya .

Sabon kwamishinan ‘yan sandan ya bukaci al’umma da su bi ka’idojin tsaro da suka hada da nisantar daukar abubuwan da ba su da amfani da za su haifar da zargi da kuma gujewa hawan dawaki da tseren motoci da tukin ganganci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...