Daga Isa Ahmad Getso
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta Jan hankalin al’ummar jihar Kano da su tabbatar sun zauna lafiya da junawa yayin bukukuwan sallah da kuma bayan sallar.
Mataimakin kwamandan Hisbah na jihar Kano Sheikh Dr Mujahid Aminudden ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da yayi da jaridar Kadaura24.
Ya ce Musulunci ya baiwa zaman lafiya muhimmanci sosai , saboda sai da zaman lafiya ake komai har Ibada da sauran harkokin na rayuwa.

Dr. Mujahid Aminudden ya bukaci matasa a kano da kada su sake su bari wani ya yi amfani da su wajen tayar da hankalin al’ummar Musulmi.
Ya ce hukumar za ta hada kai da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano baki daya.
A wata ganawa da yayi da jaridar Kadaura24, shugaban Majalisar limaman masallatan juma’a ta jihar Kano Sheikh Muhammad Nasir Adam ya bukaci limaman masallatan juma’a da su mayar da hankali wajen yin hudubobin da za su nuna muhimmanci zaman lafiya a addinin musulunci.
Ya ce jihar Kano ta na bukatar addu’o’i na musamman a yayin da za su rufe Tafsiransu na bana da kuma lokacin da suke kan mumbari.
Dalilan mu na Dakatar da Hawan Sallah a Kano – Sarki Aminu Ado Bayero
Shi ma ya bayyana zaman lafiya a matsayin ginshiƙi a addinin musulunci, don haka ya ce Allah ya la’anci duk mai ta da fitina.
Ya kuma yi godiya ga jami’an tsaro saboda gudunmawar da suke bayarwa son tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano da kasa baki daya.