Gwamnatin tarayya ta aiyana ranakun hutun Sallah

Date:

Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranakun Litinin 31 ga watan Maris da Talata 1 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun karamar Sallah.

Hakan na Ζ™unshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida wadda babbar sakatariyar ma’aikatar Magdalene Ajani ta sanya wa hannu.

InShot 20250309 102403344
Talla

A cikin sanarwar, ministan harkokin cikin gida na Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo ya buΖ™aci dukkanin Musulmai su rungumi tausayawa da karamci da zaman lafiya, inda ya jaddada muhimmancin nuna soyayya da yafiya da haΙ—in kai domin gina alumma mai cike da zaman lafiya.

Dalilan mu na Dakatar da Hawan Sallah a Kano – Sarki Aminu Ado Bayero

Ya kuma buΖ™aci alummar Musulmi su yi wa Najeriya addu’ar Ι—orewar zaman lafiya da samun ci gaba, kuma ya yi kiran gudanar da bukukuwan sallah lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related