Daga AMINU BALA
Tabbas kafafen yada labarai da su kansu’yan jarida suna da ‘yancin bayyana ra’ayoyinsu amma bisa tanadin dokoki da ka’idojin da doka ta tanada.
Zarge-zargen da ake yi a baya-bayan nan game da kamawa da tsare wasu ‘yan jarida biyu a jihar Kano ya haifar da zazzafar muhawara. Sai dai yana da kyau a daidaita al’amarin: batu na gaskiya gayyatar ‘yan jaridar 2 aka yi don su amsa wasu tambayoyi, ba wai kama su ko tsare su akai ba, kuma an gayyace su ne saboda zargin da suka yi wa Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, a wani a wata kafar yada labarai ta Internet mai suna Kano Times a wani rubutu da suka wallafa mai taken “ Gwamna Abba Kabir, ka yi hattara da Waiya”.
Wasu masu sukar sun ce gayyatar da ‘yan sanda su ka yi don yi wa yan jaridar masa tambayoyi bai dace ba. Kungiyar Amnesty International, musamman a matsayinta na babbar kungiya, ga dukkan alamu ta shiga maganar har da yin Allah wadai da gayyatar da ‘yan sanda suka yiwa yan jaridar ba tare da ta bincika abun da ya faru ba.
Yana da mahimmanci a tabbatar da gaskiyar ko menene kafin ka yanke hukunci, kuma Amnesty ba ta bincika ta sami sahihan bayanai akan batun kafin ta tofa albarkacin bakinsa wanda kuma yin hakan na daga cikin dokokin aikin jarida.

Amnesty a matsayinta ta wata babbar kungiya, na yi mamakin yadda ta kasa tantance bayanai da aka ba ta ta hanyar tuntubar hukumar da abun ya shafa, don gudun kada ta bata sunan ta. Wannan rashin yin binciken ya haifar da tambayoyi game da kokarin Amnesty International na tabbatar da gaskiya da adalci. Yana da mahimmanci a tabbatar da gaskiya kafin yanke hukunci, amma Amnesty ta yanke hukunci ba tare da bincike ba.
A wannan yanayin, haka Amnesty International ta soki gayyatar da ‘yan sanda suka yi wa mutanen biyu, kuma ta gaza bincikar hukumomin da abun ya shafa ba, don tabbatar da gaskiyar Lamari ba.
Sanin kowa ne gwamnatin jihar Kano ba ta da wata matsala da kafafen yada labarai ko ‘yan jarida. A maimakon haka, ta yarda da cewa ‘yan jarida na taka muhimmiyar rawa wajen inganta ci gaba kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar na 1999 wanda aka yiwa kwaskwarima, inda sashe na 39 (1) da (2).Bugu da kari, sashe na 22 duk sun tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida.
Dalilan mu na Dakatar da Hawan Sallah a Kano – Sarki Aminu Ado Bayero
Amnesty dole ne ta ɗauki matakai don magance irin wadancan matsaloli, ta hanyar neman sahihan labarai da tuntubar hukumomin da lamarin ya shafa don gudun sake maimaita irin waccan matsalar. Ta haka ne kawai kungiyar za ta iya dawo da martabarta a matsayin mai fafutukar kare hakkin dan Adam mara son kai.
Gwamnatin Jiha, musamman, ta amince da ‘yan jarida a matsayin manyan masu ruwa da tsaki, ginshiƙai, kuma turaku a mulkin dimokraɗiyya, hakan ta sa ta himmatu wajen tabbatar da gaskiya da riƙon amana. Haɗin kai, ba adawa ba, hanya ce ta ci gaba.
Idan Waiya yana son sauke sabon nauyin aikin da aka dora masa, ya kamata ya tsaya tsayin daka wajen sadaukar da kai da bin ka’idojin aikin jarida, ‘yancin ɗan adam, da dimokuradiyya. Jajircewarsa kan gaskiya, haɗi da gwanintar jagorancin da yake nunawa, ya sa ya zama abin koyi a aikin jarida. A matsayin Waiya na kwamishinan yada labarai aikin jarida a jihar Kano zai sami babban gata.
A ƙarshe, don taƙaita labarin,
Yana da kyau a lura cewa gwamnatin jihar Kano tana mutunta rawar da ‘yan jarida ke takawa wajen inganta ci gaba da rikon amana da kuma jajircewa wajen tabbatar da gaskiya, gwamnati na zage damtse wajen hada kai da kafafen yada labarai da ‘yan jarida domin ganin an samu ci gaba a jihar Kano.
Daga Aminu Bala Kano