Dalilan mu na Dakatar da Hawan Sallah a Kano – Sarki Aminu Ado Bayero

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Masarautar Kano karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ta dakatar da tsarin bikin hawan sallah karama.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya sanar da hakan Yana Mai bayyana cewa yin hakan ya biyo bayan wasu dalilai.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran Sarkin Abubakar Balarabe kofar Na’isa ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24.

InShot 20250309 102403344
Talla

Ya ce bayan samun shawarwari da kiraye kiraye daga shugabanni da iyaye da Malamai da kuma tattaunawa da yan Majalisar Sarki ya zama wajibi a dakatar da hawan Sallah Karama na wannan shekara.

Sarkin ya ce Hawan Sallah ba abune na ko a mutu ko ayi rai ba, Wanda idan yin hakan zai kawo tashin hankali ko hargitsi da kawo rashin zaman lafiya to ya zama wajibi a hakura dayin hawan.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce a matsayinsa na Sarkin Kano ya dauki alkawarin kiyaye Imani da mutunci da dukiya da zaman lafiyar al’umma Wanda hakan ce ta sa ya ga dacewar daukar wannan mataki domin kaucewa dukkan wani abu daka iya kawo tashin hankali ko rashin samun zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Babban Hadimin Gwamnan Kano ya rasu

A don haka ne Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’umma da sauran masoya su yi hakuri da wannan hukunci da aka zartar domin samun dorewar zaman lafiya a jihar Kano da Kuma kasa baki daya.

Sarkin na Kano ya yi amfani da wannan dama wajan kira ga al’umma da su yi amfani da lokutan bukukuwan Sallah wajan ziyartar juna domin sada zumunci, inda ya taya al’umar musulmi murna da farin cikin gudanar da azumin watan Ramadan ya na mai addu’ar samu dacewar Ubangiji daga cikin bayinsa wadanda Allah yake gafartawa dayin rahama tareda karbar ibadar da aka gudanar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...